11 Yuni 2026 - 13:27
Source: ABNA24
Iran Ta Babbake Sansanin Sojin Sama 5 A Hari Daya

Dakarun Juyin Musulunci sun hukunta sojojin ta'addancin Amurka ta hanyar kai hari kan sansanonin soji guda biyar a Jordan, Kuwait da Bahrain

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sansanin sojan sama na Muwaffaq al-Salti (Jordan) da Sansanin sojan sama na Ahmad al-Jaber (Kuwait) da Sansanin sojan sama na Ali al-Salem (Kuwait) da Hedkwatar rundunar sojan ruwa ta Amurka ta biyar (Bahrain) da Sansanin sojan sama na Sheikh Isa (Bahrain) sun sha wuta a hare—haren da Iran ta kai masu in da aka tabbatar da samun asara mai yawa na jirage da na’urori da ke girke a sansanonin.

Sabbin bayanai daga aikin leken asirin Iran a harin da aka kai wa sansanonin Amurka a Jordan da Bahrain Wata majiya mai saniya ta ce: Iran ta aiwatar da wani shiri na leken asiri da aiki mai sarkakiya don hare-haren da ta kai a safiyar ranar Alhamis kan wasu sansanonin soji na Amurka a yankin.

Hare-haren da aka ambata sun yi barna mai yawa ga kayan aikin sojojin Amurka masu tsada; ko da yake jami'an Amurka a hukumance ba su bayyana cikakken bayani game da girman wannan barnar ba har yanzu.

Wannan majiya ta soji ta ce, tun daga lokacin da jiragen Amurka manya biyu nau'in P-8 suka tashi, sojojin Iran suna lura da hanyarsu da wurin da suka sauka. An gano daya daga cikin waɗannan jiragen daga sansanin sojan sama na Diego Garcia a tsakiyar tekun Indiya, dayan kuma daga daya daga cikin sansanonin Amurka a yammacin Turai zuwa kudancin Tekun Farisa.

Dangane da bayanan da wannan majiya ta soji ta bai wa manzojinmu, wurin da waɗannan jiragen suka sauka a sansanin sojan sama na Sheikh Isa a Bahrain da sansanin Ali al-Salem a Kuwait, sun zama abin hari da makaman Iran masu daidaici da inganci.

Wata majiya kuma ta ce, Iran ta yi amfani da sa ido na leken asiri da na fili, ta lura da aƙalla jiragen yaki na F-35 na Amurka guda uku a daya daga cikin rumfunan ajiye jiragen sama na sansanin Muwaffaq al-Salti a Jordan har zuwa lokutan ƙarshe kafin harba makami mai linzami, sannan ta kai hari kan ainihin wurin wannan rumfar da makamai masu linzami masu dogon zango masu ƙarfi.

Sannan rahotanni sun cewa makamai masu linzami na tsaron Amurka bayan da suka kasa kakkabo makaman Iran masu linzami, sun fado kan wuraren zama na mutane a Bahrain wanda hakan ya haifar da asraa mai yawa da har yanzu ba bayyana hakikaninta ba.

..................

Your Comment

You are replying to: .
captcha